14/02/2023

DAULAR USMANIYYACopyright: DAULAR USMANIYYA
Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya dauki matakan gaggawa na shawo kan wahalar da jama'a ke ciki a sanadiyyar sauyin kudi domin kauce wa bore.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sultan din ya nuna takaicinsa a jiya Litinin kan lamarin inda ya nuna damuwa kan yadda jama'a s**a fada cikin yanayi na yunwa da bacin rai saboda canjin kudin.
Matsalar sauytin kudin ta kara tsananta a tsakanin jama'a bayan da rahotanni s**a nuna cewa bakuna sun daina ansar tsoffin takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000.
A ranar Laraba da ta gabata ne Kotun Kolin kasar ta hana Babban bankin kasar aiwatar da tsarinsa na hana amfani da tsofaffin kudin a ranar 10 ga watan nan na Fabarairu, har sai ta yanke hukunci a kasar da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara s**a shigar a kan lamarin.
A gobe Laraba ne Kotun Kolin ta ce za ta yanke hukunci a kan karar wadda gwamnonin jihohin uku s**a shigar.
Jihohin Kano da Naija da Ekiti da kuma Ondo suma sun bi sahun jihohin uku inda s**a shigar da kara a gaban kotun kolin kan batun sauyin kudin.