24/03/2024
A yanzu haka an lura da cewa ana buga bidiyon batsa da ake wallafawa a shafukan mutane, ba tare da saninsu ba. Masu shafin ba sa ganin su, amma wasu suna gani tamkar mai shafin ne ya wallafa. Sukan yi comments kamar kai ne kayi.
Don Allah, idan wani abu makamancin haka ya faru a kan shafina, ku sanar da ni da sauri. Haka nan na nisanta kaina daga irin waɗannan wallafar. Kaima ka aike da irin wannan sakon domin bai kamata a bari hakan ta ci gaba ba. NA GODE.
Allah ya sa mu dace .